14 Satumba 2020 - 14:17
Mali : Masu Bore Sun Yi Fatali Da Kudirin Sojoji Na Rikon Kwarya

A Mali, bangarorin da sukayi ruwa da tsaki a zanga zangar data kai ga hambarar da mulkin tsohon shugaban kasar Ibrahim Bubakar Keita, sunyi watsi da matsayar da sojoji suka cimma na yin mulkin rikon kwarya na tsawon watanni 18.

ABNA24 : Bangarorin da suka hada da kawacen ‘yan adawa da malamai da kuma kungiyoyin fara hula, sun ce basu lamunta ba da kudurorin da kwararun da sojoji suka nada suka cimma inda suka yanke tsawon lokacin watanni 18 da sojojin zasuyi na mulkin rikon kwarya kafin mika mulki ga farar hula.

Wata sanarwa da bangarorin suka fitar a jiya, ta kalubalaci abunda ta kira yunkurin kwamitin sojojin na mallakewa akan mulki.

Hakazalika a cewar kawacen na (M5-RFP), kwata kwata sanarwar bayan taron tuntuba da aka gudanar na tsawon kwanaki uku kan shirin kafa gwamnatin wucin gadi, ya yi hannun riga da ababen da aka cimma yayin taron, musamman rawar da suka taka wajen samar da canji da kuma batun masu zanga zanga da aka kashe da kuma batun farar hula da zai jagoranci mulkin rikon kwarya.

342/